Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 13:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ga mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare ta, ya ce mata, “Ga shi, ke bakarariya ce, ba ki haihuwa, amma yanzu za ki yi ciki, za ki kuwa haifi ɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare ta ya ce, “Ga shi ke bakararriya ce ba kya haihuwa, amma za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 13:3
16 Iomraidhean Croise  

Zan sa mata albarka, banda haka kuma zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za ta kuwa zama mahaifiyar al'ummai, sarakunan jama'a za su fito daga gare ta.”


Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.


Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.”


Elisha kuwa ya ce mata, “Baɗi war haka za ki rungumi ɗa na kanki.” Sai ta ce, “A'a, ya shugabana, mutumin Allah, kada fa ka yi mini ƙarya.”


sai wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, yana tsaye a dama da bagadin ƙona turare.


Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.


Don haka sai ta sheƙa a guje zuwa wurin mijinta, ta faɗa masa, “Ga mutumin da ya zo wurina ran nan, ya sāke zuwa.”


Manowa dai bai san mala'ikan Ubangiji ne ba, sai ya ce wa mala'ikan, “Ina roƙonka ka jira, mu yanka maka ɗan akuya.” Amma mala'ikan ya ce masa, “Ko na jira ba zan ci abincinku ba, amma idan kana so ka yanka, sai ka shirya hadayar ƙonawa, ka miƙa ta ga Ubangiji.”


Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala'ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba.


Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”


Mala'ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim. Ya ce wa Isra'ilawa, “Ni na kawo ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba kakanninku. Na kuma ce, ‘Ba zan ta da madawwamin alkawarina da ku ba.


Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”


Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan