Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 11:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Matar Gileyad ta haifa masa 'ya'ya maza. Sa'ad da suka yi girma, sai suka kori Yefta, suka ce masa, “Ba za ka ci gādo a gidan mahaifinmu ba, gama kai ɗan wata mace ne.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Matar Gileyad ta haifa masa ’ya’ya maza, kuma sa’ad da suka yi girma, sai suka kore Yefta, suka ce “Ba ka da gādo a cikin iyalinmu, domin kai ɗan wata mace ce.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 11:2
10 Iomraidhean Croise  

A lokacin nan ana yunwa a ƙasar. Sai Abram ya tafi Masar baƙunci, gama yunwa ta tsananta a ƙasar.


Sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori wannan baiwa da ɗanta, gama ɗan baiwan nan ba zai zama magaji tare da ɗana Ishaku ba.”


Za a nisantar da kai daga mazinaciya, wadda take ƙoƙari ta lalatar da kai da daɗin bakinta,


Ɗana, don me za ka fi son matar wani? Don me za ka bar matar wani ta lallame ka da daɗin bakinta?


Leɓunan matar wani, mai yiwuwa ne, su yi zaƙi kamar zuma, sumbace-sumbacenta kuma su fi man zaitun taushi.


Amma me Nassin ya ce? “Ka kori kuyangar da ɗanta, don ko kaɗan ɗan kuyangar ba zai ci gādo tare da ɗan 'ya ba.”


“Shege ba zai shiga taron jama'ar Ubangiji ba. Har tsara ta goma zuriyarsa ba za su shiga taron jama'ar Ubangiji ba.


Yefta mutumin Gileyad ne, shi kuwa jarumi ne, amma mahaifiyarsa karuwa ce. Gileyad ne mahaifinsa.


Sai Yefta ya gudu daga wurin 'yan'uwansa, ya zauna a ƙasar Tob. 'Yan iska kuwa suka taru wurin Yefta, sukan tafi yawo tare da shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan