Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 10:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Yana da 'ya'ya maza guda talatin, waɗanda suke hawan jakai talatin. Suna kuma da birane talatin a ƙasar Gileyad, waɗanda har yanzu ake kira biranen alfarwai. Ana kiran biranen Hawwot-Yayir, wato na Yayir.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Yana ’ya’ya talatin, waɗanda suke hawan jakuna talatin. Sun shugabanci birane talatin a Gileyad, har wa yau ana ce da biranen Hawwot Yayir.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 10:4
8 Iomraidhean Croise  

Sarki kuwa ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo abubuwan nan?” Ziba ya amsa, ya ce, “An kawo wa iyalin sarki jakuna su hau, da abinci, da 'ya'yan itace, domin samari su ci, ruwan inabi kuma domin waɗanda suke rafkewa a jejin su sha.”


Ki yi murna ƙwarai, ya Sihiyona! Ta da murya ya Urushalima! Ga Sarkinki yana zuwa wurinki, Shi mai adalci ne, mai nasara, Shi kuma mai tawali'u ne, Yana bisa kan jaki, a kan aholaki.


Yayir, ɗan Manassa, ya tafi ya ci ƙauyukansu da yaƙi, suka ba su suna Hawot-yayir.


(Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)


Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu.


Yayir ya rasu aka binne shi a Kamon.


Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas.


Ku ba da labari, Ku da kuke haye da fararen jakuna, Kuna zaune a shimfiɗu, Ku da dole ku tafi da ƙafa duk inda za ku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan