Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mahukunta 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sa’ad da Yahuda ya fāɗa musu, Ubangiji kuwa ya ba da Kan’aniyawa da Ferizziyawa a hannunsu, suka kuwa kashe mutum dubu goma a Bezek.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mahukunta 1:4
17 Iomraidhean Croise  

Da ya zo gaban sarki, sai sarki ya ce masa, “Mikaiya, mu tafi Ramot don yaƙi, ko kuwa kada mu tafi?” Ya amsa masa ya ce, “Ka haura, za ka yi nasara, Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Yadda kai da kanka ka kori arna, Ka dasa jama'arka a ƙasarsu, Yadda ka hori sauran al'umma, Amma ka sa jama'arka su wadata.


Ya kori mazaunan wurin sa'ad da jama'arsa suka dirkako, Ya rarraba ƙasar ga kabilan Isra'ila, A nan ya ba su izini su zauna a wurin, a cikin alfarwansu.


Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.


Yau za ku sani Ubangiji Allahnku yake muku ja gaba sa'ad da kuke hayewa. Shi wuta ne mai cinyewa, zai hallaka su, ya rinjayar muku su, domin ku kore su, ku hallaka su nan da nan kamar yadda Ubangiji ya alkawarta muku.


Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.


Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa.


Yefta ya haye zuwa wurin Ammonawa domin ya yi yaƙi da su. Ubangiji kuwa ya ba da su a hannunsa.


Saboda haka jama'ar Isra'ila suka zauna tare da Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Amoriyawa, da Ferizziyawa, da Hiwiyawa, da Yebusiyawa.


Sa'ad da Saul ya tara mutane a Bezek, aka sami mutum dubu ɗari uku (300,000) daga Isra'ila, dubu talatin (30,000) kuma daga Yahuza.


Amma idan sun ce, ‘Ku haura zuwa wurinmu,’ to, sai mu haura, gama wannan alama ce, wato Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan