Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Rana Kabila Shugaba Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.