Mahukunta 1:1 - Littafi Mai Tsarki1 Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?” Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20201 Bayan da Yoshuwa ya rasu, Isra’ilawa suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne zai fara tafiya don yă yaƙi Kan’aniyawa dominmu?” Faic an caibideil |
Suka sāke yin tambaya ga Ubangiji suka ce, “Mu sāke tafiya mu yi yaƙi da 'yan'uwanmu, mutanen Biliyaminu, ko kuwa mu bari?” Ubangiji kuwa ya ce musu, “Ku je, gama gobe zan ba da su gare ku.” A lokacin nan akwatin alkawari na Ubangiji yana nan. Finehas ɗan Ele'azara, ɗan Haruna, shi ne mai aiki a gabansa.