Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 9:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ya kuma ce musu, “Kada ku ɗauki wani guzuri a tafiyarku, ko sanda, ko burgami, ko gurasa, ko kuɗi. Kada kuma ku ɗauki taguwa biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 9:3
12 Iomraidhean Croise  

Ka dogara ga Ubangiji ka aikata nagarta, Ka zauna a ƙasar, ka sami lafiya.


Sai ya kira goma sha biyun nan, ya fara aikensu biyu-biyu, ya kuma ba su iko a kan baƙaƙen aljannu.


Sai ya ce wa almajiransa, “Don haka, ina gaya muku, kada ku damu da batun rayuwarku game da abin da za ku ci, ko kuma jikinku, abin da za ku yi sutura.


To, ga shi Allah yana ƙawata tsire-tsiren jeji ma haka, waɗanda yau suke a raye, gobe kuwa a jefa su a murhu, balle ku? Ya ku masu ƙarancin bangaskiya!


Ya kuma ce musu, “Sa'ad da na aike ku ba kuɗi a ɗamararku, ba burgami, ba takalma, akwai abin da kuka rasa?” Suka ce, “Babu.”


Ya amsa musu ya ce, “Duk mai taguwa biyu, ya raba da marar ita, mai abinci ma haka.”


Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su.


Duk gidan da kuka sauka, ku zauna a nan har ku tashi.


Ai, ba sojan da yake a bakin dāga da ransa zai sarƙafe da sha'anin duniya, tun da yake burinsa shi ne yă faranta wa wanda ya ɗauke shi soja.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan