Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 8:3 - Littafi Mai Tsarki

3 da Yuwana matar Kuza, wakilin Hirudus, da Suzanatu, da kuma waɗansu da yawa da suka yi musu ɗawainiya da kayansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 8:3
19 Iomraidhean Croise  

“Amma wane ni ko kuma jama'ata, da za mu iya kawo sadaka mai yawa haka? Gama dukan kome daga gare ka yake. Daga cikin abin da muka karɓa daga wurinka muka ba ka.


Kuɗin da ta samu ta kasuwanci za a keɓe wa Ubangiji. Ba za ta tara wa kanta ba, amma waɗanda suke yi wa Ubangiji sujada su za su yi amfani da kuɗinta don su saya wa kansu abinci da sutura da suke bukata.


A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.


Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.


To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,


Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga ɗan yaron, tare da uwa tasa Maryamu, suka fāɗi gabansa suka yi masa sujada. Sa'an nan suka kwance kayansu, suka miƙa masa gaisuwar zinariya, da lubban, da mur.


Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’


Sai Sarkin zai amsa musu ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, tun da yake kun yi wa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan'uwana mafi ƙanƙanta, ai, ni kuka yi wa.’


Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba.


Akwai kuma waɗansu mata da yawa a can suna hange daga nesa, waɗanda suka biyo Yesu tun daga ƙasar Galili, suna yi masa hidima.


To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa.


Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da yake ciki.


To, a Ikkilisiyar da take Antakiya akwai waɗansu annabawa, da masu koyarwa, wato Barnaba, da Saminu wanda ake kira Baƙi, da Lukiyas Bakurane, da Manayan wanda aka goya tare da sarki Hirudus, da kuma Shawulu.


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


Dukan tsarkaka suna gai da ku, tun ba ma na fadar Kaisar ba.


wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan