Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 8:2 - Littafi Mai Tsarki

2 da waɗansu mata da aka raba da baƙaƙen aljannu da kuma rashin lafiyarsu. Cikinsu da Maryamu mai suna Magadaliya, wadda aka fitar wa da aljannu bakwai,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 8:2
11 Iomraidhean Croise  

Ta haka ya shahara a cikin duk ƙasar Suriya. Aka kuwa kakkawo masa dukan marasa lafiya, masu fama da cuta iri iri, da masu shan azaba, da kuma masu aljannu, da masu farraɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.


Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa.


[Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai.


Sai taron mutane masu yawan gaske suka bi shi, da waɗansu mata da suke kuka, suke kuma gunji saboda shi.


Amma duk idon sani, da kuma matan da suka biyo shi, tun daga ƙasar Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban waɗannan abubuwa.


Matan nan kuwa da suka zo tare da shi daga ƙasar Galili, suka bi baya, suka duba kabarin da yadda kuma aka sa jikinsa.


Sai Yesu ya tambaye shi, “Yaya sunanka?” Ya ce, “Tuli,” don aljannu da yawa sun shiga cikinsa.


Haka fa sojan suka yi. To, kusa da gicciyen Yesu kuwa da uwa tasa, da 'yar'uwa tata, da Maryamu matar Kilofas, da kuma Maryamu Magadaliya, suna tsaye.


Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan