Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 8:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ba da daɗewa ba Yesu ya zazzaga birni da ƙauye yana wa'azi, yana yin bisharar Mulkin Allah. Sha biyun nan kuwa suna tare da shi,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 8:1
18 Iomraidhean Croise  

Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.


Wanda duk ya ji Maganar Mulki bai kuma fahimce ta ba, sai Mugun ya zo ya zăre abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya faɗa a hanya.


Sai ya zazzaga duk ƙasar Galili, yana koyarwa a majami'unsu, yana shelar bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiya na mutane.


Sai Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami'unsu, yana yin bisharar Mulkin Allah, yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.


Ya gama ƙasar Galili duk yana wa'azi a majami'unsu, yana kuma fitar wa mutane aljannu.


Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra'ila.


Wata rana yana koyar da mutane a Haikali, yana yi musu bishara, sai ga manyan firistoci da malaman Attaura, da shugabanni suka matso,


“Ruhun Ubangiji yana tare da ni, Domin yā shafe ni in yi wa matalauta bishara. Ya aiko ni in yi shelar saki ga ɗaurarru, In kuma buɗe wa makafi ido, In kuma 'yanta waɗanda suke a danne,


Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Mu ma mun kawo muku albishir, cewa, alkawarin nan da Allah ya yi wa kakanninmu,


Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan