Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake cewa, “ ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Yesu ya amsa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 4:8
14 Iomraidhean Croise  

Sai ku ji tsoron Ubangiji Allahnku. Shi ne za ku bauta masa, ku rantse da sunansa.


Sai kuma ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku bauta masa. Ku manne masa, ku yi rantsuwa da sunansa.


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada, amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka, waɗanda suke shaidar Yesu. Allah za ka yi wa sujada.” Domin gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.


Ka sa su sani kai kaɗai ne Ubangiji, Kai kaɗai ne mamallakin dukan duniya!


Amma, sai ya ce mini, “Ko kusa kada ka yi haka! Ni abokin bautarku ne, kai da 'yan'uwanka annabawa, da kuma waɗanda suke kiyaye maganar littafin nan. Allah za ka yi wa sujada.”


Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.


Yesu ya amsa masa ya ce, “A rubuce yake, ‘Ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba.’ ”


Sa'an nan Sama'ila ya ce wa mutanen Isra'ila, “Idan da zuciya ɗaya kuke komowa wurin Ubangiji, to, sai ku rabu da baƙin alloli, da gumakan nan Ashtarot. Ku sa zuciyarku ga bin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai, shi kuwa zai cece ku daga hannun Filistiyawa.”


Ku yi tsayayya da shi, kuna dagewa a kan bangaskiyarku, da yake kun san 'yan'uwanku a duniya duka an ɗora musu irin wannan shan wuya.


Amma Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka yi nesa da ni, ya Shaiɗan! Tarko kake a gare ni. Ba ka tattalin al'amuran Allah, sai dai na mutane.”


Rana tana zuwa sa'ad da girmankan 'yan adam zai ƙare, zai kuma lalatar da fāriyar 'yan adam. Sa'an nan Ubangiji ne kaɗai za a ɗaukaka.


Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.


In kuwa za ka yi mini sujada, duk su zama naka.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan