Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 4:2 - Littafi Mai Tsarki

2 har kwana arba'in, Iblis yana gwada shi. A kwanakin nan bai ci kome ba. Da suka ƙare kuwa ya ji yunwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 4:2
16 Iomraidhean Croise  

Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”


Sai Iliya ya tashi ya ci abinci ya sha ruwa ya sami ƙarfi, sa'an nan ya kama tafiya kwana arba'in dare da rana har zuwa Horeb, wato dutsen Allah.


“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”


Sai Musa ya shiga girgijen, ya hau bisa dutsen. Ya zauna a kan dutsen yini arba'in da dare arba'in.


Musa kuwa yana tare da Ubangiji yini arba'in da dare arba'in, bai ci ba, bai sha ba. Sai ya rubuta kalmomin alkawarin a kan allunan, wato dokokin nan goma.


Sai ya aika wa mutanen Nineba da sanarwa cewa, “Wannan doka ce daga sarki da majalisarsa. Kada kowa ya ci wani abu, mutane, da shanu, da tumaki, da awaki duka, kada kowa ya ci, ko ya sha ruwa.


Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.


Da ya yi azumi kwana arba'in ba dare ba rana, daga baya yunwa ta kama shi.


Iblis ya ce masa, “In dai kai Ɗan Allah ne, ka umarci dutsen nan ya zama gurasa,”


Rijiyar Yakubu kuwa a nan take. Saboda gajiyar tafiya fa, sai Yesu ya zauna haka nan a bakin rijiyar. Wajen tsakar rana ce kuwa.


Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.


“Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku.


Sa'ad da na hau kan dutsen domin in karɓo allunan dutse, wato allunan alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, na zauna a kan dutsen dare arba'in da yini arba'in ban ci ba, ban sha ba.


Tun da yake shi ma ya sha wuya, sa'ad da aka gwada shi, ashe, zai taimaki waɗanda ake yi wa gwaji.


Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba.


Goliyat yana ta tsokanar Isra'ilawa safe da maraice, har kwana arba'in.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan