Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 3:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ko yanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin itatuwa. Saboda haka duk itacen da bai yi 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare shi, a jefa a wuta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 3:9
14 Iomraidhean Croise  

“A cikin itatuwan Aidan, da wa za a kamanta darajarka da girmanka? Duk da haka za a kai ka lahira tare da itatuwan Aidan. Za ka zauna tare da marasa kaciya, da waɗanda aka kashe da takobi. Wannan Fir'auna ke nan, da dukan jama'arsa, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Sai ya yi magana da ƙarfi, ya ce, “ ‘A sare itacen, a daddatse rassansa, A zage ganyayensa ƙaƙaf, a warwatsar da 'ya'yansa. A sa namomin jeji su gudu daga ƙarƙashinsa, Tsuntsaye kuma su tashi daga rassansa.


Ka kuma ga mai tsaro tsattsarka yana saukowa daga sama, yana cewa a sare itacen nan, a ragargaje shi, amma a bar kututturen da saiwoyinsa cikin ƙasa ɗaure da sarƙar baƙin ƙarfe da tagulla. An ce a bar shi can a ɗanyar ciyawar saura, ya jiƙe da raɓa, ya zauna tare da namomin jeji har shekara bakwai.


Koyanzu ma an ɗora bakin gatari a gindin bishiya. Saboda haka duk bishiyar da bata bada 'ya'ya masu kyau ba, sai a sare ta a jefa a wuta.


Duk itacen da ba ya 'ya'ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta.


Sai ya ba su misalin nan ya ce, “Wani mutum yana da ɓaure a garkar inabinsa. Sai ya zo neman 'ya'ya, amma bai samu ba.


Sai ya ce wa mai kula da garkar, ‘Ka ga, yau shekara uku ke nan nake zuwa neman 'ya'yan wannan ɓaure, amma ba na samu. A sare shi. Ƙaƙa zai tsare wuri a banza?’


In ya yi 'ya'ya, to, in kuwa bai yi ba, sai a sare.’ ”


Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.


Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku.


domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan