Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 a zamanin da Hanana da Kayafa suke manyan firistoci, Maganar Allah ta zaike wa Yahaya ɗan Zakariya a jeji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 3:2
21 Iomraidhean Croise  

Murya tana kira tana cewa, “Ka shirya hanya a jeji domin Ubangiji! Ka share hanya a hamada domin Allahnmu!


wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,


Ubangiji ya ce mini,


Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.


Ana nan sai Ubangiji ya yi magana da Yunusa, ɗan Amittai, ya ce,


Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima.


Ubangiji ya yi magana da Zafaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza.


Sun tafi ke nan, sai Yesu ya fara yi wa taro maganar Yahaya, ya ce, “Kallon me kuka je yi a jeji? Kyauron da iska take kaɗawa?


Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa.


Yadda yake a rubuce a littafin Annabi Ishaya cewa, “Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba, Wanda zai shirya maka hanya.


Sai ɗan yaron ya girma, ya ƙarfafa a ruhu. Ya kuwa zauna a jeji har ranar bayyanarsa ga Isra'ila.


Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”


Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.


tare da Hanana, babban firist, da Kayafa, da Yahaya, da Iskandari, da kuma duk waɗanda suke dangin babban firist.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan