Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 3:1 - Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tibariyas, Buntus Bilatus yana mulkin Yahudiya, Hirudus yana sarautar Galili, ɗan'uwansa Filibus yana sarauta Ituriya da Tarakunitas, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiliya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 3:1
19 Iomraidhean Croise  

Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i.


A lokacin nan sarki Hirudus ya ji labarin shaharar Yesu.


Don dā ma Hirudus ya kama Yahaya ya ɗaure shi, ya sa shi kurkuku saboda Hirudiya, matar ɗan'uwansa Filibus.


To, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, sai 'yar Hirudiya ta yi rawa a gaban taron, har ta gamshi Hirudus,


To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”


Sai suka ɗaure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga mai mulki Bilatus.


Don dā Hirudus da kansa ya aika aka kamo Yahaya, ya ɗaure shi a kurkuku saboda Hirudiya matar ɗan'uwansa Filibus, wadda shi Hirudus ya aura.


Amma wani sanadi ya zo, da ranar haihuwar Hirudus ta kewayo, ya yi wa hakimansa, da sarakunan yaƙinsa, da kuma manyan ƙasar Galili biki.


Nan take waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce masa, “Ai, sai ka tashi, ka fita daga nan, gama Hirudus yana son kashe ka.”


A kwanakin nan Kaisar Augustas ya yi shela, cewa a rubuta dukkan mutanen da suke ƙarƙashin mulkinsa.


Sai Bilatus ya zartar da hukunci a biya musu bukata.


Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi,


To, sarki Hirudus ya ji duk abin da ake yi, ya kuwa damu ƙwarai, don waɗansu suna cewa Yahaya ne aka tasa daga matattu.


“Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.


Amma bayan shekara biyu sai Borkiyas Festas ya gāji Filikus. Filikus kuwa don neman farin jini a wurin Yahudawa, ya bar Bulus a ɗaure.


Sai sarki ya tashi, haka kuma mai mulki da Barniki, da waɗanda suke a zaune tare da su.


Gama hakika Hirudus da Buntus Bilatus sun haɗa kai a birnin nan tare da al'ummai da jama'ar Isra'ila gāba da Yesu Baranka mai tsarki, wanda ka maishe shi Almasihu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan