Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 2:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 2:9
27 Iomraidhean Croise  

har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.


Sa'ad da Haruna yake magana da taron jama'ar, suka duba wajen jeji, sai ga ɗaukakar Ubangiji ta bayyana a cikin girgije.


Da safe za ku ga ɗaukakar Ubangiji, gama ya ji gunagunin da kuka yi a kansa, gama wane, mu, da za ku yi gunaguni a kanmu?”


Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, Ya ga girmansa da ikonsa.


Sa'an nan za a bayyana ɗaukakar Ubangiji, Dukan 'yan adam kuwa za su gan ta. Ubangiji ne kansa ya yi wannan alkawari.”


Ki tashi, ya Urushalima, ki haskaka kamar rana, Daukakar Ubangiji tana haskakawa a kanki kamar rana!


Sai na tashi na tafi na tsaya a fili, sai ga ɗaukakar Ubangiji a wurin, a tsaye kamar ɗaukakar da na gani a bakin kogin Kebar. Sai na fāɗi rubda ciki.


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


Sai mala'ikan ya je wurinta, ya ce, “Salama alaikun, yake zaɓaɓɓiya, Ubangiji yana tare da ke!”


A wannan yankin ƙasa kuwa waɗansu makiyaya suna kwana a filin Allah, suna tsaron garken tumakinsu da dad dare.


Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.


Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa.


sai ga mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka ɗakin, sa'an nan mala'ikan ya bugi Bitrus a kwiɓi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarƙar ta zube daga hannunsa.


Don a daren jiya wani mala'ikan Allah wanda ni nasa ne, nake kuma bauta masa, ya tsaya kusa da ni,


Amma da daddare sai wani mala'ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun, ya fito da su, ya ce,


Mu dukanmu kuma, fuskokinmu ba lulluɓi, muna nuna ɗaukakar Ubangiji, kamar madubi, ana sauya mu mu ɗauki kamanninsa cikin ɗaukaka mai hauhawa. Ubangiji kuwa wanda yake ruhu, yana zartar da haka.


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.”


Bayan haka, na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, mai iko da yawa, sai aka haskaka duniya da ɗaukakarsa.


Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan