Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 17:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ku kula da kanku fa. In ɗan'uwanka ya yi laifi, ka tsauta masa. In kuwa ya tuba, ka yafe shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka, ku lura da kanku. “In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 17:3
18 Iomraidhean Croise  

Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri, Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai, Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.


Ku fa kula da kanku, kada ku kuskura, ku ƙulla alkawari da mazaunan ƙasar inda za ku tafi, don kada su zama muku alƙalai.


Mutum mai fasaha yakan koyi abu da yawa daga tsautawa ɗaya, fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.


Gara ka tsauta wa mutum a fili da ka bar shi ya zaci ba ka kula da shi ba sam.


Faufau kada ka kuskura ka kwaɓi mai fāriya, zai ƙi ka saboda wannan, amma idan ka kwaɓi mai hikima zai girmama ka.


“Kada wani ya riƙe ɗan'uwansa da ƙiyayya a zuciyarsa, amma ya daidaita rashin jituwa da shi, don kada ya yi zunubi saboda shi.


Sai Bitrus ya matso ya ce masa, “Ya Ubangiji, sau nawa ɗan'uwana zai yi mini laifi in yafe masa? Har sau bakwai?”


“Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.


Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.


“Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.


Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.


“Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su,


Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,


Ya ku 'yan'uwana, in waninku ya bauɗe wa gaskiya, wani kuma ya komo da shi,


Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan