Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 16:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Sai wakilin ya ce a ransa, ‘Ƙaƙa zan yi, da yake maigida zai karɓe wakilci daga hannuna? Ga shi, ba ni da ƙarfin noma, in yi roƙo kuwa, ina jin kunya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 “Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 16:3
26 Iomraidhean Croise  

Da shigowar Haman, sai sarki ya ce masa, “Me za a yi wa mutumin da sarki yake so ya ɗaukaka?” Haman ya yi tunani ya ce a ransa, “Wane ne sarki yake so ya ɗaukaka, in banda ni?”


Rago yakan ƙosa ya sami wani abu ainun, amma sam, ba zai samu ba. Mai mai da hankali ga aikinsa zai sami kowane abu da yake bukata.


Idan kai rago ne za ka gamu da wahala a ko'ina, amma idan kai amintacce ne, ba za ka sha wahala ba.


Rago yana daidai da mutumin da yake lalatar da abubuwa.


Rago, yi ta ragwancinka ka yi ta sharar barci, amma kai za ka sha yunwa.


Manomin da ya cika lalaci, ya kasa nome gonakinsa a kan kari, a lokacin girbi ba zai sami kome ba.


Baran da aka shagwaɓa tun yana yaro, a ƙarshe zai ɗauki kansa tankar magājin gida.


Me za ku yi sa'ad Allah zai hukunta ku? Me za ku yi kuma sa'ad da ya kawo muku masifa daga wata ƙasa mai nisa? Ina za ku sheƙa neman taimako? A ina kuma za ku ɓoye dukiyarku?


Annabawa sun yi annabcin ƙarya, Firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, Mutanena kuwa suna so haka! Amma sa'ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?”


Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar idi? Da a ranar idin Ubangiji?


Da magariba ta yi, mai garkar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kirawo ma'aikatan, ka biya su hakkinsu, ka fara daga na ƙarshe har zuwa na farko.’


Sai suka iso Yariko. Yana fita daga Yariko ke nan, da shi, da almajiransa, da wani ƙasaitaccen taro, sai ga wani makaho mai bara, wai shi Bartimawas, ɗan Timawas, yana zaune a gefen hanya.


Sai ya ce a ransa, ‘To, ƙaƙa zan yi? Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonata.’


Sai ya kira shi ya ce masa, ‘Labarin me nake ji naka? Kawo lissafin wakilcinka, don ba sauran ka zama wakilina.’


An kuma ajiye wani gajiyayye a ƙofarsa, mai suna Li'azaru, wanda duk jikinsa miki ne.


Ana nan sai gajiyayyen nan ya mutu, mala'iku kuma suka ɗauke shi, suka kai shi wurin Ibraham. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.


Yauwa! Na san abin da zan yi, don in an fisshe ni daga wakilcin, mutane su karɓe ni a gidajensu.’


Da fari ya ƙi, amma daga baya sai ya ce a ransa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane,


Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Ashe, ba wannan ne yakan zauna yana bara ba?”


sai ga wani mutum da aka haifa gurgu, ana ɗauke da shi. Kowace rana kuwa akan ajiye shi a ƙofar Haikali, wadda ake kira Ƙawatacciyar Ƙofa, don ya roƙi sadaka ga masu shiga Haikali.


Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”


Gama mun ji labari cewa waɗansunku malalata ne kawai, ba sa aikin kome, masu shisshigi ne kurum.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan