Sai ku fahimci ma'anar wannan tukuna, ‘Ni kam, zaman jinƙai nake nema a gare ku, ba hadaya ba.’ Ba domin in kira masu adalci na zo ba, sai dai masu zunubi.”
Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.”
Su kuwa da suka ji haka, suka ɗaukaka Allah. Suka ce wa Bulus, “To, kā gani ɗan'uwa, dubban mutane sun ba da gaskiya a cikin Yahudawa, dukansu kuwa masu himma ne wajen bin Shari'a.