3 Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku halaka kamarsu.
3 Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.
Daga nan ya je ya ɗebo waɗansu aljannu bakwai da suka fi shi mugunta. Sai su shiga su zauna a wurin. Wannan mutum ƙarshen zamansa ya fi na fari lalacewa. Haka zai zamar wa wannan mugun zamani.”
Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.
yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”
Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galilawa sun fi duk sauran Galilawa zunubi ne, don sun sha wannan azaba?
Ko kuwa goma sha takwas ɗin nan da hasumiya ta faɗo a kansu, a Siluwam, ta kashe su, kuna tsammani sun fi duk sauran mutanen Urushalima laifi ne?
Ina gaya muku ba haka ba ne! In kuwa ba ku tuba ba, duk za ku hallaka kamarsu.”
a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.
Saboda haka sai ku tuba, ku juyo, domin a shafe zunubanku, Ubangiji kuma kansa ya riƙa wartsakar da ku,