Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 11:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Sai ya ce musu, “In kuna addu'a ku ce, “ ‘Ya Uba, a kiyaye sunanka da tsarki, Mulkinka yă zo,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Sai ya ce musu, “Sa’ad da kuke yin addu’a ku ce, “ ‘Ya Uba, sunanka mai tsarki ne mulkinka ya zo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 11:2
45 Iomraidhean Croise  

sai ka kasa kunne ga addu'arsa. Ka ji daga Sama, wurin zamanka, ka amsa masa abin da ya roƙe ka, domin dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma yi tsoronka kamar jama'arka, Isra'ilawa, domin kuma su sani wannan Haikali da na gina wurin da za a yi maka sujada ne.


Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”


ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na kakanninmu, kai ne Allah na cikin Sama, kai ne kuma kake mulkin dukan al'umman duniya. A gare ka iko da ƙarfi suke, don haka ba wanda ya isa ya jā da kai.


Ku yabi Ubangiji, ku ƙarfafa, ku manyan mala'iku, Ku da kuke biyayya da umarnansa, Kuna kasa kunne ga maganarsa!


Ya Allah, ka bayyana girmanka a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!


Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Yana da kursiyinsa a Sama. Yana kallon dukan mutane Yana sane da abin da suke yi.


Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama, Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!


Yi tunani kafin ka yi magana, kada ka yi wa Allah wa'adi na gaggawa. Allah yana Sama kai kuwa kana duniya. Don haka kada ka faɗa fiye da abin da ya kamata.


Kai ne Ubanmu. Ko kakanninmu, wato su Ibrahim da Yakubu, ba za su iya taimakonmu ba, amma kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu. Kai ne Mai Fansarmu a koyaushe.


Zan ɗauki fansa saboda sunana mai tsarki, mai girma, wanda aka ɓata a wurin al'ummai, ku kuma kuka ɓata shi a cikinsu. Al'ummai kuwa za su sani ni ne Ubangiji sa'ad da na tabbatar da tsarkina a wurinku a kan idonsu.


Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan.


A kwanakin waɗannan sarakuna, Allah na Sama zai kafa wani mulki wanda ba zai taɓa rushewa ba har abada, ba kuma za a gādar da shi ga waɗansu mutane ba. Wannan mulki zai ragargaje dukan waɗannan mulkoki, ya kawo ƙarshensu. Wannan mulki zai dawwama har abada.


Amma tsarkaka na Maɗaukaki za su karɓi mulki, su kuwa riƙe mulkin har abada abadin.


Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’


Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi, Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu, Ka karɓe mu saboda alherinka, Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.


Musa kuwa ya ce wa Haruna, “Wannan ita ce ma'anar abin da Ubangiji yake cewa, ‘Dukan waɗanda suke bauta mini, dole su nuna ladabi ga tsarkina, zan kuma bayyana ɗaukakata ga jama'ata.’ ” Haruna kuwa ya yi tsit.


Kwa iya ba da dabba, marar cikakkiyar halitta don hadaya ta yardar rai, amma ba za ku bayar don hadaya ta cika wa'adi ba, ba za a karɓa ba.


Duniya za ta cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, Kamar yadda ruwa ya cika teku.


“Kowa ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin Sama.


yana cewa, “Ku tuba, domin Mulkin Sama ya kusato.”


To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”


Wata rana Yesu yana addu'a a wani wuri. Bayan da ya gama, sai wani a cikin almajiransa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka koya mana addu'a, kamar yadda Yahaya ya koya wa almajiransa.”


Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu. Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Ai, ruhun da kuka samu ba na bauta ba ne, har da za ku koma zaman tsoro. A'a, na zaman 'ya'ya ne, har muna kira, “Ya Abba! Uba!”


Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin yă cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu.


Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.


Alheri da salama na Allah ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu, su tabbata a gare ku.


Ɗaukaka tā tabbata ga Allahnmu, Ubanmu, har abada abadin. Amin! Amin!


zuwa ga tsarkaka da amintattun 'yan'uwa cikin Almasihu da suke a Kolosi. Alheri da salamar Allah Ubanmu su tabbata a gare ku.


Daga Bulus, da Sila, da Timoti, zuwa ga Ikkilisiyar Tasalonikawa, wadda take ta Allah uba da Ubangiji Yesu Almasihu. Alheri da salama su tabbata a gare ku.


ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.


To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Ubangiji, Ya kuma ɗaukaka sunanka? Domin kai kaɗai ne Mai Tsarki. Dukkan al'ummai za su zo su yi maka sujada, Don ayyukanka na adalci sun bayyana.”


Sai na ji kamar wata sowar ƙasaitaccen taro, kamar ƙugin ruwa mai gudu, kamar aradu mai ƙara, suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki shi ne yake mulki.


Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan