Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.
Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.