Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 10:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 10:1
14 Iomraidhean Croise  

Dattawan Isra'ila saba'in suna tsaye a gabansu. Yazaniya ɗan Shafan yana tsaye tare da su. Kowa yana riƙe da farantin ƙona turare. Hayaƙin turaren ya tunnuƙe zuwa sama.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Tattaro mini mutum saba'in daga cikin dattawan Isra'ila waɗanda aka sani su ne dattawa da shugabannin jama'ar, ka kawo su a alfarwa ta sujada, ka sa su tsaya tare da kai.


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


Kai kuma, ɗan yarona, za a ce da kai annabin Maɗaukaki, Gama za ka riga Ubangiji gaba, Domin ka shisshirya hanyoyinsa,


Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”


Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”


Sai ya aiki jakadu su riga shi gaba, suka kuwa tafi suka shiga wani ƙauyen Samariyawa su shisshirya masa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan