Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 1:9 - Littafi Mai Tsarki

9 bisa ga al'adar hidimar firistoci, sai kuri'a ta nuna shi ne mai shiga Haikalin Ubangiji, ya ƙona turare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 1:9
10 Iomraidhean Croise  

'Ya'yan Amram, maza, su ne Haruna, da Musa. Aka keɓe Haruna domin ya tsarkake abubuwa mafi tsarki, domin shi da 'ya'yansa za su ƙone turare a gaban Ubangiji, su yi masa hidima, su riƙa sa albarka da sunansa har abada.


Amma Haruna da 'ya'yansa maza suka miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa, da kan bagaden ƙona turare, domin dukan aikin Wuri Mafi Tsarki, da kuma yin kafara domin Isra'ila bisa ga dukan abin da Musa, bawan Allah, ya umarta.


Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.


'Ya'yana, kada ku yi sakaci, gama Ubangiji ne ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa, ku yi masa hidima, ku ƙona masa turare.”


Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.


Sai ya watsar da kuɗin azurfan nan a Haikali, ya fita, ya je ya rataye kansa.


In an gama waɗannan shirye-shirye haka, sai firistoci kullum su riƙa shiga sashin farko an alfarwar, suna hidimarsu ta ibada.


Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan