Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Amma ba su da ɗa, don Alisabatu bakararriya ce, dukansu biyu kuma sun tsufa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 1:7
16 Iomraidhean Croise  

Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”


Ga shi kuwa, Ibrahim da Saratu sun tsufa, sun kwana biyu, gama Saratu ta daina al'adar mata.


Ishaku kuwa ya yi addu'a sai matarsa Rifkatu ta yi ciki.


Sa'ad da Rahila ta ga ba ta haihuwa, sai ta ji kishin 'yar'uwarta, ta kuma ce wa Yakubu, “Ka ba ni 'ya'ya, in kuwa ba haka ba, zan mutu!”


Sarki Dawuda ya tsufa ƙwarai, don haka ko an rufe shi da abin rufa ba ya jin ɗumi.


Elisha ya ce, “To, me za a yi mata?” Sai Gehazi ya amsa ya ce, “Ai, ba ta da ɗa, mijinta kuwa tsoho ne.”


A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.


Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


Ana nan, wata rana Zakariya na kan hidima tasa ta firist, a sa'ad da hidimar ta kewayo kan ƙungiyarsu,


Bangaskiyarsa kuwa ba ta raunana ba, bai dubi gajiyawar jikinsa ba, don yana da shekara wajen ɗari a lokacin, ko kuma cewa Saratu ta wuce haihuwa.


Ta wurin bangaskiya Saratu da kanta ta sami ikon yin ciki, ko da yake ta wuce lokacin haihuwa, tun da dai ta amince, cewa shi mai yin alkawarin nan amintacce ne.


Yana da mata biyu, sunayensu Hannatu da Feninna. Feninna tana da 'ya'ya, amma Hannatu ba ta haihuwa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan