An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al'amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani.
Duk da haka dai a taron ikkilisiya na gwammace in faɗi kalmomi biyar a game da tunanina, domin in karantar da waɗansu, da in faɗi kalmomi dubu goma da wani harshe.