Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 1:2
25 Iomraidhean Croise  

Farkon bisharar Yesu Almasihu, Ɗan Allah, ke nan.


Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


Mai shukan nan fa Maganar Allah yake shukawa.


Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.


Ku ma shaidu ne, domin tun farko kuke tare da ni.


Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin in lokacinsu ya yi ku tuna na faɗa muku.” “Ban faɗa muku abubuwan nan tun da farko ba, domin ina tare da ku.


Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.


Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”


Da kuma suka faɗi Maganar a Bariyata, suka tafi Ataliya.


Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.


To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.


Amma tashi ka miƙe tsaye, gama na bayyana a gare ka ne da wannan maƙasudi, wato in sa ka mai hidima, mashaidi kuma na abubuwan da ka gani a game da ni, da kuma abubuwa waɗanda zan bayyana maka a nan gaba.


Domin mu kam, ba yadda za a yi sai mun faɗi abin da muka ji, muka kuma gani.”


To, waɗanda aka warwatsar nan kuwa, suka yi ta zazzagawa suna yin bishara.


da ya sa ni bawan Almasihu Yesu ga al'ummai, ina hidimar bisharar Allah, domin al'ummai su zama hadaya mai karɓuwa a gare shi, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.


Ta haka ya kamata a san mu da zama ma'aikatan Almasihu, masu riƙon amanar asirtattun al'amuran Allah.


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


Don haka, ku dattawan ikkilisiya da suke cikinku, ni da nike dattijon ikkilisiya, ɗan'uwanku, mashaidin shan wuyar Almasihu, mai samun rabo kuma a cikin ɗaukakar da za a bayyana, ina yi muku gargaɗi,


Ai, ba tatsuniyoyi da aka ƙaga da wayo muka bi ba, sa'ad da muka sanar da ku ikon Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma bayyanarsa, ɗaukakarsa ce muka gani muraran.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan