Kada kowa ya kasance cikin alfarwar sujada lokacin da Haruna ya shiga Wuri Mafi Tsarki domin ya yi kafara don kansa, da gidansa, da dukan taron jama'ar Isra'ila, sai lokacin da ya fita.
Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
Ga kuma wani mala'ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu'o'in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin.