Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Luka 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da suka tabbata a cikinmu,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Luka 1:1
13 Iomraidhean Croise  

Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]


Amma an rubuta waɗannan ne, domin ku ba da gaskiya Yesu shi ne Almasihu, Ɗan Allah, ta wurin gaskatawa kuma ku sami rai a cikin sunansa.


Wani yakan ɗaukaka wata rana fiye da sauran ranaku, wani kuwa duk ɗaya ne a wurinsa. Kowa dai yă zauna a cikin haƙƙaƙewa, a kan ra'ayinsa.


yana haƙƙaƙewa, cewa Allah na da ikon yin abin da ya yi alkawari.


Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu,


Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.


domin bishararmu ba da magana kawai ta zo muku ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma matuƙar tabbatarwa. Kun dai san irin zaman da muka yi a cikinku domin ku amfana,


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya ba ni ƙarfin sanar da bishara sosai da sosai, domin duk al'ummai su ji, aka kuwa cece ni daga bakin zaki.


sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.


Muna dai bukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa ƙarshe,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan