Ƙidaya 4:4 - Littafi Mai Tsarki4 Wannan shi ne aikin 'ya'yan Kohat, maza, a cikin alfarwa ta sujada a kan abubuwa mafi tsarki. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20204 “Ga aikin Kohatawa a Tentin Sujada, kulawa da kayayyaki mafi tsarki. Faic an caibideil |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.