Ƙidaya 4:3 - Littafi Mai Tsarki3 su ƙidaya daga mai shekara talatin zuwa hamsin, wato waɗanda suka isa su yi aiki a alfarwa ta sujada. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Ku ƙidaya dukan maza daga shekara talatin zuwa hamsin da suka zo domin aiki a Tentin Sujada. Faic an caibideil |
A watan biyu na shekararsu ta biyu da suka komo wurin Haikalin Allah a Urushalima, sai Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa ɗan Yehozadak, da sauran 'yan'uwansu firistoci, da Lawiyawa da dukan waɗanda suka komo Urushalima daga bauta suka fara aikin ginin. Suka sa Lawiyawa 'yan shekara ashirin zuwa gaba su yi shugabancin aikin ginin Haikalin Ubangiji.