Ga shi kuma, ni da kaina, na sa Oholiyab ɗan Ahisamak na kabilar Dan tare da shi, na kuma sa hikima a zukatan masu hikima, don su yi dukan abin da na umarce ka
Za su zama masu hidima a cikin wurina mai tsarki, suna lura da ƙofofin Haikali, suna hidima a cikin Haikalin. Za su yanka hadayar ƙonawa da ta sadaka domin mutane. Za su lura da mutanen, su yi musu hidima.
Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi.