Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 32:4 - Littafi Mai Tsarki

4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban taron jama'a, ƙasa ce mai kyau don dabbobi. Ga shi kuwa, barorinka suna da dabbobi da yawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 ƙasar da Ubangiji ya ci da yaƙi a gaban mutane Isra’ila, suna da kyau don dabbobi, bayinku kuma suna da dabbobi.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 32:4
9 Iomraidhean Croise  

Waɗannan da aka lasafta sunayensu, su ne suka zo a kwanakin Hezekiya Sarkin Yahuza, suka fāɗa wa alfarwai da bukkoki waɗanda suka tarar a can, suka hallaka su sarai, sa'an nan suka maye wurinsu saboda akwai makiyaya domin garkunansu a wurin.


Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad.


Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā.


Isra'ilawa kuwa suka karkashe su da takobi, suka mallaki ƙasarsa tun daga Kogin Arnon zuwa Kogin Yabbok, har zuwa kan iyakar Ammonawa, gama Yahaza ita ce kan iyakar Ammonawa.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama'arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.”


Haka fa suka kashe shi, shi da 'ya'yansa maza, da dukan jama'arsa, har ba wanda ya tsira, suka kuwa mallaki ƙasarsa.


Idan mun sami tagomashi a gare ka, ka ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu, kada ka kai mu a wancan hayin Urdun.”


Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan