Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 24:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da Bal'amu ya gane Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra'ilawa albarka bai tafi neman shawara kamar dā ba, sai ya fuskanci jeji,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 To, da Bala’am ya ga cewa Ubangiji yana jin daɗin sa wa Isra’ila albarka, bai koma wajen sihiri kamar dā ba, amma ya juya fuskarsa wajen hamada.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 24:1
13 Iomraidhean Croise  

Da safe Bal'amu ya tashi, ya ce wa dattawan Balak, “Ku koma ƙasarku, gama Ubangiji bai yarda mini in tafi tare da ku ba.”


Dattawan Mowab da na Madayana suka ɗauki kafin alkalami suka tafi wurin Bal'amu suka faɗa masa saƙon Balak.


Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya nan kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa in tafi in sadu da Ubangiji a can.”


Ga shi, an umarce ni in sa albarka. Ya sa albarka, ba zan iya janye ta ba.


Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’


Balak kuwa ya kai Bal'amu a ƙwanƙolin Dutsen Feyor wanda yake fuskantar hamada.


Sai Bal'amu ya ce wa Balak, “Tsaya kusa da hadayarka ta ƙonawa, ni kuwa zan tafi can, in ga ko Ubangiji zai sadu da ni. Duk abin da ya bayyana mini, zan faɗa maka.” Ya kuwa tafi wani faƙo a kan tudu.


Balak ya yi yadda Bal'amu ya faɗa masa. Ya miƙa bijimi da rago a kan kowane bagade.


Ku tuna fa, su ne, ta wurin shawarar Bal'amu, suka yaudari Isra'ilawa, suka saɓi Ubangiji cikin maƙidar Feyor, har annoba ta fasu a jama'ar Ubangiji.


Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.


Yanzu kuwa na sani za ka zama sarki, sarautar Isra'ila za ta kahu a hannunka.


Saul kuwa ya tashi ya tafi jejin Zif tare da zaɓaɓɓu dubu uku (3,000) na Isra'ila don ya nemi Dawuda.


Sai Saul ya ce wa Dawuda, “Ubangiji ya sa maka albarka, ɗana Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, ka kuwa yi nasara!” Dawuda dai ya yi tafiyarsa, Saul kuma ya koma gidansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan