Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 21:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ubangiji kuwa ya ji wa'adin Isra'ilawa, ya kuwa ba su Kan'aniyawa, suka hallaka su da biranensu ƙaƙaf. Don haka aka sa wa wurin suna Horma, wato hallakarwa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 21:3
11 Iomraidhean Croise  

Za ka saurara ga addu'o'in masu kaɗaici, ya Ubangiji, Za ka ba su ƙarfin hali.


Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita, Zai kuwa ji addu'arta.


Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina, Yana kasa kunne ga addu'o'ina.


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Sai Amalekawa da Kan'aniyawa, mazauna a kan tudun, suka gangaro, suka ci su, suka runtume su har Harma, wato hallakarwa.


Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.


“Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.


da Sarkin Horma, da Sarkin Arad,


da Eltola, da Kesil, da Horma,


Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.


da Horma, da Ashan, da Atak,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan