Ƙidaya 2:3 - Littafi Mai Tsarki3-9 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka 186,400 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya. Faic an caibideilSabon Rai Don Kowa 20203 Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab. Faic an caibideil |
Waɗannan su ne mutanen da aka zaɓa. Kabila Shugaban Kabila Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Yahuza Nashon ɗan Amminadab Issaka Netanel ɗan Zuwar Zabaluna Eliyab ɗan Helon Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Ashiru Fagiyel ɗan Okran Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Naftali Ahira ɗan Enan
Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Rana Kabila Shugaba Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.