Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 13:3 - Littafi Mai Tsarki

3-15 Musa kuwa ya yi biyayya, daga jejin Faran ya aika da waɗannan shugabanni, Shammuwa ɗan Zakkur, daga kabilar Ra'ubainu. Shafat ɗan Hori, daga kabilar Saminu. Kalibu ɗan Yefunne, daga kabilar Yahuza. Igal ɗan Yusufu, daga kabilar Issaka. Hosheya ɗan Nun, daga kabilar Ifraimu. Falti ɗan Rafu, daga kabilar Biliyaminu. Gaddiyel ɗan Sodi, daga kabilar Zabaluna. Gaddi ɗan Susi, daga kabilar Manassa. Ammiyel ɗan Gemalli, daga kabilar Dan. Setur ɗan Maikel, daga kabilar Ashiru. Nabi ɗan Wofsi, daga kabilar Naftali. Geyuwel ɗan Maci, daga kabilar Gad.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka bisa ga umarnin Ubangiji, Musa ya aike su daga Hamadan Faran. Dukansu kuwa shugabanni ne na Isra’ilawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 13:3
11 Iomraidhean Croise  

Isra'ilawa kuwa suka tashi daki-daki daga jejin Sinai. Girgijen kuma ya tsaya a jejin Faran.


Bayan wannan jama'a suka tashi daga Hazerot suka sauka a jejin Faran.


“Ka aiki mutane su leƙi asirin ƙasar Kan'ana wadda nake ba Isra'ilawa. Daga kowace kabila na kakanninsu, ka zaɓi mutum guda wanda yake shugaba a cikinsu.”


Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.


Haka iyayenku suka yi sa'ad da na aike su daga Kadesh-barneya don su dubo ƙasar.


“Ga sunayen mutanen da za su taimake ka raba gādon ƙasar, Ele'azara firist, da Joshuwa ɗan Nun.


“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.


“Na ga al'amarin ya gamshe ni, saboda haka na ɗauki mutum goma sha biyu daga cikinku, mutum guda daga kowace kabila.


Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.


Sama'ila kuwa ya rasu. Dukan Isra'ilawa suka taru suka yi makoki dominsa. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Faran.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan