Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 1:51 - Littafi Mai Tsarki

51 Sa'ad da kuka tashi tafiya, Lawiyawa za su kwankwance alfarwar, su ne kuma za su kafa ta, su ɗaɗɗaure, idan suka sauka a sabon wuri. Idan wani dabam ya zo kusa da alfarwar za a kashe shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 Duk sa’ad da za a gusar da tabanakul, Lawiyawa ne za su saukar da shi; kuma duk sa’ad da za a kafa shi, Lawiyawa ne za su yi haka. Duk wani dabam da ya je kusa da shi za a kashe shi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 1:51
15 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari.


A rana ta ashirin ga watan biyu a shekara ta biyu, sai aka gusar da girgijen daga kan alfarwa ta sujada.


Zai zama abin tunawa ga Isra'ilawa domin kada wanda ba firist ba, ba kuwa a cikin zuriyar Haruna ba, ya guso don ya ƙona turare a gaban Ubangiji, domin kada ya zama kamar Kora da ƙungiyarsa. Haka Ubangiji ya faɗa wa Ele'azara ta bakin Musa.


Duk wanda ya kusaci alfarwa ta sujada ta Ubangiji, zai mutu. Ashe, dukanmu za mu mutu ke nan!”


Mutumin da sandansa ya yi toho, shi ne na zaɓa, da haka zan sa gunagunin da Isra'ilawa suke yi a kaina ya ƙare.”


Nan gaba kada Isra'ilawa su zo kusa da alfarwa ta sujada don kada su yi zunubi, su mutu.


Za su taimake ku, su kuma yi dukan ayyukan alfarwa. Amma fa, ba za su kusaci kayayyakin Wuri Mai Tsarki, ko bagade ba, don kada su, har da ku, ku mutu.


Za su haɗa kai da ku su lura da alfarwa ta sujada da dukan aikace-aikace na cikin alfarwar. Kada wani dabam ya kusace ku.


Da kai, da 'ya'yanka za ku yi aikin firist da duk abin da ya shafi bagade da aiki na bayan labule. Ku ne za ku yi wannan aiki. Na ba ku aikin firist ya zama naku. Duk wani dabam wanda ya zo kuwa, za a kashe shi.”


Ka sa Haruna da 'ya'yansa maza, su kula da aikinsu na firist, idan kuwa wani mutum dabam ya yi ƙoƙarin yin wannan aiki, to, za a kashe shi.”


Waɗanda za su yi zango a gaban alfarwa ta sujada daga gabas, su ne Musa, da Haruna da 'ya'yansa maza, waɗanda aka danƙa musu tafiyar da aikin Wuri Mai Tsarki, da dukan aikin da za a yi wa Isra'ilawa. Banda su, duk wanda ya je kusa da wurin sai a kashe shi.


Sai Ubangiji ya kashe mutum saba'in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan