Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 1:4
19 Iomraidhean Croise  

Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.


Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki.


Ka rubuta sunan Haruna a kan sandan Lawi, gama akwai sanda guda domin kowane gidan kakanninsu.


Sunan Ba'isra'ilen da aka kashe tare da Bamadayaniyar, Zimri ɗan Salu, shi ne shugaban gidan Saminawa.


Ya ce wa Musa, “Ɗauki sugabannin jama'a, ka rataye su a rana a gabana don in huce daga fushin da nake yi da Isra'ilawa.”


Musa ya kuma ce wa shugabannin kabilan Isra'ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.”


Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).


Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,


Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.


Shugabanni goma suka tafi tare da shi, shugaba ɗaya daga kowace kabilar Isra'ila. Kowane ɗayansu shugaba ne a danginsa a kabilar Isra'ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan