Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Ƙidaya 1:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Waɗannan shugabannin kabilai waɗanda suke manya cikin kabilansu, an zaɓe su daga cikin jama'a domin wannan aiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Ƙidaya 1:16
20 Iomraidhean Croise  

Ka kuma zaɓa daga cikin jama'a isassun mutane, masu tsoron Allah, amintattu, waɗanda suke ƙyamar cin hanci. Ka naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


Sai Musa ya zaɓi isassun mutane daga cikin Isra'ilawa ya naɗa su shugabannin jama'a na dubu dubu, da na ɗari ɗari, da na hamsin hamsin, da na goma goma.


“Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Musa da Haruna suka ɗauki waɗannan mutane goma sha biyu,


Ku roƙi shugaban kowace kabila ya taimake ku.”


Amma idan ɗaya kaɗai aka busa, sai shugabannin Isra'ila su tattaru a wurinka.


Ni kuwa zan sauko, in yi magana da kai a can. Zan ɗiba daga cikin ruhun da yake cikinka, in ba su. Su kuma za su ɗauki nawayar jama'ar tare da kai, domin kada ka ɗauki nawayar kai kaɗai.


'Ya'yan Eliyab, maza su ne Yemuwel, da Datan, da Abiram. Datan da Abiram ne aka zaɓa daga cikin taron jama'ar, suna cikin ƙungiyar Kora wadda ta tayar wa Musa da Haruna, har ma da Ubangiji.


Musa ya kuma ce wa shugabannin kabilan Isra'ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.”


Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,


Don haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma'amala da jama'a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu dubu, waɗansu a kan ɗari ɗari, waɗansu a kan hamsin hamsin, waɗansu kuma a kan goma goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.


Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”


Sai ya ce wa fādawan da suke tsaye kewaye da shi, “Ku ji, ya ku mutanen Biliyaminu, ɗan Yesse zai ba kowannenku gonaki, da gonakin inabi ne? Zai maishe ku shugabanni na dubu dubu, da na ɗari ɗari, har da dukanku kuka yi mini maƙarƙashiya? Ba wanda ya sanar da ni sa'ad da ɗana ya haɗa kai da ɗan Yesse? Ba wanda ya damu saboda da ni, balle a faɗa mini yadda ɗana ya kuta barana ya tayar mini, yana fakona, kamar yadda yake a yau?”


Ku lura sosai da dukan wuraren da yake ɓuya, sa'an nan ku komo mini da tabbataccen labari. Sa'an nan zan tafi tare da ku. Idan yana ƙasar, zan neme shi ko'ina a ƙasar Yahuza.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan