Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Irmiya 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 da a zamanin Yehoyakim ɗan Yosiya Sarkin Yahuza kuma, har ƙarshen shekara ta goma sha ɗaya ta Zadakiya ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, har zuwa lokacin da aka kai mazaunan Urushalima zaman talala a wata na biyar.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Irmiya 1:3
19 Iomraidhean Croise  

Sai Fir'auna-neko ya sarautar da Eliyakim ɗan Yosiya a matsayin tsohonsa. Ya sāke masa suna ya sa masa suna Yehoyakim. Ya ɗauki Yehowahaz ya tafi da shi Masar, can ya mutu.


Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya naɗa Mattaniya ɗan'uwan tsohon Yekoniya sarki a maimakon Yekoniya sa'an nan ya ba shi suna Zadakiya.


'Ya'yan Yosiya, maza, su ne Yohenan ɗan farinsa, na biyu shi ne Eliyakim, na uku shi ne Zadakiya, na huɗu shi ne Yehowahaz,


Ubangiji ya yi magana da ni, ya ce,


Ubangiji ya yi magana da Irmiya sa'ad da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, da dukan sojojinsa, da dukan sojojin mulkokin al'umman da suke a ƙarƙashinsa, da dukan mutane suke yaƙi da Urushalima da dukan biranenta.


A lokacin da Yehoyakim, ɗan Yosiya yake mulkin Yahuza, sai Ubangiji ya ce wa Irmiya,


“Ka ɗauki takarda, ka rubuta dukan maganar da na yi maka a kan Isra'ila, da Yahuza, da dukan al'ummai, tun daga ran da na fara yi maka magana a zamanin Yosiya har ya zuwa yau.


A rana ta tara ga watan huɗu, a shekara ta goma sha ɗaya ta sarautar Zadakiya, sai aka huda garun birnin.


in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa'ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba'in, saboda ni ne kuka yi azumin?


“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan