Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Hosiya 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Yezreyel, gama ba da daɗewa ba zan ziyarci gidan Yehu da hukunci saboda jinin da ya zubar a Yezreyel. Zan sa mulkin Isra'ila ya ƙare.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Hosiya 1:4
32 Iomraidhean Croise  

Ahab yana da 'ya'ya maza saba'in a Samariya, sai Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika zuwa Samariya wurin shugabanni da dattawan birni, da masu lura da 'ya'yan Ahab.


Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.


A zamanin Feka Sarkin Isra'ila, sai Tiglat-filesar mai mulkin Assuriya, ya zo ya ci Iyon, da Abel-bet-ma'aka, da Yanowa, da Kedesh, da Hazor, da Gileyad, da Galili, da dukan ƙasar Naftali. Sa'an nan ya kwashe mutane zuwa bauta a Assuriya.


A shekara ta talatin da takwas ta sarautar Azariya Sarkin Yahuza, Zakariya ɗan Yerobowam na biyu, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya wata shida.


Yanzu fa, Ubangiji kansa zai ba ku alama. Wata budurwa wadda take da ciki, za ta haifi ɗa, za a raɗa masa suna Immanuwel.


Bayan wannan na yi jima'i da matata annabiya. Ta ɗauki ciki, ta haifi ɗa namiji, Ubangiji ya ce mini, “Ka raɗa masa suna, ‘Kwashe ganima nan da nan, washe da hanzari.’


Ga shi, an haifa mana ɗa! Mun sami yaro! Shi zai zama Mai Mulkinmu. Za a kira shi, “Mashawarci Mai Al'ajabi,” “Allah Maɗaukaki,” “Uba Madawwami,” “Sarkin Salama.”


Kashegari sa'ad da Fashur ya fitar da Irmiya daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashur ba, amma ya ba ka suna Magormissabib, wato razana ta kowace fuska.


Haka Ubangiji Allah na Isra'ila ya faɗa a kan makiyayan jama'arsa. “Kun warwatsar da garkena kun kore su, ba ku lura da su ba. Ni ma haka zan yi da ku saboda muguntarku, ni Ubangiji na faɗa.


Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci.


Waɗannan suka tsiraita ta, suka kama 'ya'yanta mata da maza, suka kashe ta da takobi. Sai ta zama abin karin magana a wurin mata sa'ad da aka hukunta ta.


Kin bi halin 'yar'uwarki, domin haka zan hukunta ki kamar yadda na hukunta ta.’ ”


Gomer ta kuma ɗauki ciki, ta haifi 'ya mace. Ubangiji kuma ya ce wa Yusha'u, “Ka raɗa mata suna Bajinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama'ar Isra'ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.


Ubangiji kuma ya ce masa, “Ka raɗa masa suna, Ba-mutanena-ba-ne, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.


Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al. A kwanakin nan takan ƙona musu turare, Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai, Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.” In ji Ubangiji.


Ƙasa kuma za ta amsa wa hatsi, da ruwan inabi, da mai, Su ma za su amsa wa Yezreyel.


Allahna zai ƙi su Domin ba su yi masa biyayya ba. Za su zama masu yawo cikin al'ummai.


Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba.


Za ta haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”


Amma mala'ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro Zakariya, an karɓi addu'arka, matarka Alisabatu za ta haifa maka ɗa, za ka kuma sa masa suna Yahaya.


Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu.


Sai ya nema a ba shi allo, sa'an nan ya rubuta, “Sunansa Yahaya.” Duka suka yi mamaki.


Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.


Garuruwan da suke cikin yankin ƙasar su ne, Yezreyel, da Kesullot, da Shunem,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan