Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Haggai 1:9 - Littafi Mai Tsarki

9 “Kun sa zuciya za ku sami da yawa, sai kuka sami kaɗan. Sa'ad da kuma kuka kawo shi gida, sai na hurar da shi. Me ya sa haka? Saboda Haikalina da yake zaman kufai, amma ko wannenku yana fama da ginin gidansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 “Ga shi, kukan sa rai za ku sami da yawa, amma sai ku ga kun sami kaɗan. Ɗan kaɗan ɗin ma da kukan kawo gida, nakan hura shi yă tafi. Me ya sa yake faruwa haka?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda gidana da yake zaman kango, yayinda kowannenku yana faman gina gidansa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Haggai 1:9
25 Iomraidhean Croise  

A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”


An bayyana ƙarƙashin teku a fili, An tone tussan duniya, Lokacin da Ubangiji ya yi wa abokan gāba tsautawa, Ya yi musu ruri cikin fushi.


Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa da zai ji jita-jita, har ya koma ƙasarsa, zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”


Kada ka hukunta ni, ya Allah. Ka faɗa mini laifin da kake tuhumata da shi.


Waɗansu mutane sukan kashe kuɗinsu hannu sake, duk da haka arzikinsu sai ƙaruwa yake yi. Waɗansu kuwa saboda yawan tsumulmularsu sukan talauce.


Muradin mutum kamar lahira yake, a kullum ba ya ƙoshi.


Kowane abu yana sa gajiya, Gajiyar kuwa ta fi gaban magana. Idanunmu ba sā ƙoshi da gani, Haka kuma kunnuwanmu ba sā ƙoshi da ji.


Ciyawa takan bushe, furanni kuma sukan yi yaushi Sa'ad da Ubangiji ya aiko da iska ta hura ta kansu. Mutane kuwa ba su fi ciyawa ƙarfi ba!


Kadada biyar na gonar inabi za ta ba da kwalaba shida kaɗai na ruwan inabi. Garwa ashirin na iri za su ba da tsabar hatsi garwa biyu!”


Sun shuka alkama, sun girbe ƙayayuwa, Sun gajiyar da kansu, amma ba su amfana da kome ba. Za su sha kunya saboda abin da suke girbe, Saboda zafin fushin Ubangiji.”


Zan zubo maka da fushina, in hura maka wutar fushina. Zan bashe ka a hannun mugaye, gwanayen hallakarwa.


Amma a shekara ta biyar, sai ku ci 'ya'yan itatuwan domin su ba ku amfani a yalwace. Ni ne Ubangiji Allahnku.


“Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi wa rufin katako, amma Haikalin nan yana zaman kufai?


Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”


Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


“Za ku shuka iri da yawa a gonakinku, amma kaɗan za ku girbe gama fara za su cinye.


Amma ga laifinka, wato, ka yar da ƙaunar da ka yi tun daga farko.


Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan