Haggai kuwa, da Zakariya ɗan Iddo, annabawa, suka yi wa Yahudawan da suke a Yahuza da Urushalima wa'azi da sunan Allah na Isra'ila wanda yake iko da su.
A rana ta fari ga watan shida a shekara ta biyu ta sarautar sarki Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Haggai, cewa ya yi magana da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, mai mulkin Yahuza, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.