Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Na yi farin ciki ƙwarai, zuciyata kuma ta ƙarfafa saboda ƙaunar da kake yi, yă kai 'dan'uwana, domin zukatan tsarkaka sun wartsake ta dalilinka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:7
11 Iomraidhean Croise  

Sun dai wartsakar da ni da kuma ku. Sai ku kula da irin waɗannan mutane.


Saboda haka ne zukatanmu suka ƙarfafa. Banda ƙarfafa zukatanmu kuma, har wa yau mun ƙara farin ciki ƙwarai, saboda farin cikin Titus, don dukanku kun wartsakar da shi.


Na amince da ku ƙwarai, ina kuma taƙama da ku gaya. Zuciyata ta ƙarfafa ƙwarai. Duk da wahalce-wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.


ba ma fāsa tunawa da aikinku na bangaskiya a gaban Allahnmu, Ubanmu, da famar da kuke yi domin ƙauna, da kuma begen ku mara gushewa ga Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Saboda wannan ne kuma muke gode wa Allah ba fasawa, domin sa'ad da kuka karɓi Maganar Allah ta bakinmu, ba ku karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, Maganar Allah, wadda take aiki a cikin zuciyarku, ku masu ba da gasikya.


Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?


Wace irin godiya za mu yi wa Allah saboda ku, a kan matuƙar farin cikin da muke yi a gaban Allahnmu ta dalilinku!


Ubangiji yă yi wa iyalin Onisifaras jinƙai, don sau da yawa yake sanyaya mini zuciya, bai kuwa ji kunyar ɗaurina da aka yi ba.


Ya ɗan'uwana, ka yarda in sami wata fa'ida a gare ka saboda Ubangiji! Ka sanyaya mini zuciya saboda Almasihu.


Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu 'ya'yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan