Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ina addu'a bangaskiyar nan da ta haɗa ku, tă kasance mai ƙwazo a wajen ciyar da sanin dukkan kyawawan abubuwan da suke namu, saboda Almasihu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:6
18 Iomraidhean Croise  

Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.


To, haskenku yă riƙa haskakawa haka a gaban mutane, domin su ga kyawawan ayyukanku, su kuma ɗaukaka Ubanku da yake cikin Sama.”


asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.


Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.


Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.


Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,


kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.


Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.


Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.


Ya ku 'yan'uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa?


Haka ma, bangaskiya ita kaɗai, ba tare da aikin da ya nuna ta ba, banza ce.


Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.


Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,


Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.


In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan