Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.
Titus kuwa, ai, abokin tarayyata ne, abokin aikina kuma game da al'amuranku. 'Yan'uwan nan namu kuwa, ai, manzanni ne na ikilisiyoyi, masu ɗaukaka Almasihu.
Ya kai abokin bautata na hakika, ina roƙonka, ka taimaki matan nan, don sun yi fama tare da ni a al'amarin bishara, haka ma Kilemas da sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suke a rubuce a cikin Littafin Rai.
Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.