Aristarkus, abokin ɗaurina, yana gaishe ku, haka kuma Markus, wanda kakansu ɗaya ne da Barnaba. Shi ne aka riga aka yi muku umarni a game da shi. In dai ya zo wurinku, ku karɓe shi.
Abafaras wanda yake ɗaya daga cikinku, bawan Almasihu Yesu, yana gaishe ku, a kullum yana yi muku addu'a da himma, ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.