Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Har wa yau kuma, ka shirya mini masauki, domin ina sa zuciya a ba ni yarjin zuwa gare ku albarkacin addu'arku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:22
13 Iomraidhean Croise  

ya ce, ‘Kada ka ji tsoro Bulus, lalle za ka tsaya a gaban Kaisar, ga shi kuma, Allah ya amsa ya yardar maka duk abokan tafiyarka su tsira.’


Da suka sa masa rana, sai suka zo masaukinsa, su da yawa. Sa'an nan ya yi ta yi musu bayani, yana ta shaidar musu Mulkin Allah, tun daga safe har magariba, yana ƙoƙarin rinjayarsu a kan Yesu, ta hanyar Attaurar Musa da littattafan annabawa.


ina sa zuciya in gan ku, in zan wuce zuwa ƙasar Asbaniya, har ma ku raka ni zuwa can, bayan da na ɗan ɗebe kewa da ganinku.


Ku ma sai ku taimake mu da addu'a, domin mutane da yawa su gode wa Allah, ta dalilinmu, saboda albarkar da aka yi mana, ta amsa addu'o'i masu yawa.


Domin na san duk wannan zai zama sanadin lafiyata, ta wurin addu'arku da taimakon Ruhun Yesu Almasihu.


Na kuma amince har ga Ubangiji, ni ma da kaina ina zuwa ba da daɗewa ba.


Musamman nake tsananta roƙonku ku yi haka, don a hanzarta a komo da ni a gare ku.


Ku sani, an sāki ɗanuwanmu Timoti, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri.


Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke.


Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan