Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Filemon 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Ni Bulus, ni nake rubuto wannan da hannuna, ni kuwa zan biya, kada ma a yi zancen ranka da na fanso maka!

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Filemon 1:19
14 Iomraidhean Croise  

Na ɗauki lamuninsa, a hannuna za ka neme shi. Idan ban komo maka da shi, in kawo shi a gabanka ba, bari alhakin ya zauna a kaina har abada,


Ni Tartiyas, mai rubuta wasiƙar nan, ina gaishe ku saboda Ubangiji.


Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.


Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,


Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă san ta, ya kuma karanta ta.


Don kada ya zamana in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba ku shirya ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.


To, ni Bulus, ina gaya muku, in kuna yarda a yi muku kaciya, Almasihu ba zai amfane ku kome ba ke nan.


Ku dubi irin rubutu gwada-gwada da nake muku da hannuna!


zuwa ga Timoti, ɗana na hakika, ta wajen bangaskiya. Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.


zuwa ga Titus, ɗana na hakika ta wajen bangaskiyarmu mu duka. Alheri da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Mai Cetonmu su tabbata a gare ka.


Ko ma ya yi maka wani laifi, ko kuwa kana binsa wani abu, sai ka mai da shi a kaina.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan